Kamfanin dillancin labaran Ahl al-Bait (AS) - ABNA ya habarta cewa, bayan sake aukuwar harin ta'addanci a haramin Shahcheragh, Ahmad bin Al-Musa Al-Kazem, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Majalisar Ahlul Baiti (A.S.) ta Duniya ta fitar da sanarwa ta sakon ta'aziyya.
Sakon sanarwar da ta'aziyya shine kamar haka:
Da sunan Allah Qasemul Jabareen
Daga Allah mu ke kuma gareshi zamu koma
بسم الله قاصم الجبارین
انا لله و انا الیه راجعون
A kwanakin karshe na watan Muharram da kuma lokacin da iyalan gidan manzon Allah (s.a.w) suke zaman makoki da juyayi, masoya da mabiya Imaman Athar (a.s) a Iran din Musulunci suna tunawa da irin wahalhalun da Ayarin Ashura suka sha, sun kasance cikin zaman makoki da ruku'u ga ibadar Ubangiji, sannan a sannu a hankali suna masu shirya kansu domin halartar taron Tattakin Arbaeen Husaini na kasa da kasa, kwatsam aka sake kai farmakin matsorata na harin ta'addanci a hubbaren Shahcheragh (amincin Allah ya tabbata a gare shi). a Shiraz hakan ya haifar da bakin ciki mai yawa da kuma shahadar da mai hidami ga wannan harami Harim Malik Pasban bisa zalunci tare da raunata maziyarta da dama na magoya bayan Sharifai a hubbaren Ahlulbaiti na uku, ya kara sabunta bakincikinmu da dukkan 'yan uwa musulmi na Iran da masoyanmu na kasashen waje.
Ko shakka babu irin wannan yunkuri na rashin basira na zalunci wata alama ce ta yanke kauna da makiya Musulunci daga yada munanan take-take da tsare-tsarensu, da kuma tsananin bacin rai da nuna kiyayya dangane da tasiri da 'ya'yan da tsarin tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran mai tsarki ke da shi a cikin kowane lungu na duniya, kuma hakika yana kawo haske, da yawan ma'abota imani da al'ummar Iran za su sami kariya daga Musulunci da juyin juya halin Musulunci; Domin mu al'ummar Imam Husaini (AS) ne kuma al'ummar shahada, kuma darajarmu ita ce shahada.
Majalisar Ahlul-baiti ta duniya a yayin da take mika ta'aziyyarta da jimaminta ga wannan lamari mai daci tana mai mika ta'aiyyaarta ga halarar Waliyul As Allah ya kara masa yarda, ya kuma gaggauta fitowarsa ga Jagoran Juyin juya halin musulunci Allah ya tsare shi ya tsawaita rayuwarsa ga kuma al'ummar Iran masu daraja da ma'abota kishin wannan majalissar Ahlul-baiti na duniya, tana mai yakinin cewa hukumar tsaro masu tabbatar da doka da oda ta kasar da kwamandoji zasu kokarin hukunta duk wadanda suka aikata wannan ta'addanci da kuma masu hannu a wannan ta'addanci akan ayyukansu na wulakanci cikin gaggawa za kuma su yi ƙoƙari don hana sake afkuwar irin wannan harin tare da magance irin wannan a nan gaba.
«و سیعلم الذین ظلموا ای منقلب ینقلبون»
Majalisar Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su).